3 Janairu 2021 - 10:02
An Sake Kashe Sojojin Faransa Biyu A Mali

Fadar shugaban kasa a Faransa, ta sanar da mutuwar sojojin kasar biyu da suka hada da mace guda a yankin Menaka na kasar Mali.

ABNA24 : A cewar sanarwar da farar Elysée, ta fitar, sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da motar da suka ciki ta fuskanci hari daga wani abun fashewa a daidai lokacin da tawagarsu ke sintiri a yankin na Menaka ranar Asabar.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya ce ya kadu matuka game da mutuwar sojojin biyu.

Wanna harin dai na zuwa ne kwana biyar bayan wani makamancinsa da ya yi sanadin mutuwar sojojin faranasar uku ranar Litini data gabata a kasar ta Mali, wanda wata kungiya dake da alaka da Al’Qaida ta dauki alhakin kaiwa a wata sanarwa data fitar a jiya.

Mutuwar sojojin Faransar biyu na baya bayan nan ya sanya adadin sojojin faransa da aka kashe a yankin Sahel ya kai 49, tun bayan da faransa ta sanya kafa a yankin a cikin shekara 2013.

342/*